GOMNAN JIHAR GOMBE YA KAFA KWAMITIN KARTAKWANA DON FARFADO DA BANGAREN LAFIYA
23/01/2024 Gwamnan Jihar Gombe Ya Kafa Kwamitin Kartakwana Don Farfaɗo Da Ɓangaren Lafiya Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya kafa kwamitin farfaɗo da fannin kiwon lafiya a jihar, inda Farfesa Aliyu Usman El-Nafaty zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba. Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar, yana mai cewa kwamitin ya ƙunshi mambobin da aka zaɓo bisa kwazo, aminci da biyayyarsu. Mambobin sun haɗa da: Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko Ta Jihar Gombe Dr. Abdulrahman Shuaibu, da Babban Sakataren Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Gombe (Go-Health) Dokta Abubakar Musa, da Dr. Mohammed Garba Buwa daga Ma’aikatar Lafiya, da Architect. Yakubu Mamman daga Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri, da Mohammed Bappa daga Hukumar Kula da Harkokin Kiwon Lafiya ta Jihar Gombe. Sauran sun haɗa da QS Ahmed Mohammed Kabir, Mai Bada Shawara kan sayayyan kayayyaki, da...