GOMNAN JIHAR GOMBE YA KAFA KWAMITIN KARTAKWANA DON FARFADO DA BANGAREN LAFIYA
23/01/2024
Gwamnan Jihar Gombe Ya Kafa Kwamitin Kartakwana Don Farfaɗo Da Ɓangaren Lafiya
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya kafa kwamitin farfaɗo da fannin kiwon lafiya a jihar, inda Farfesa Aliyu Usman El-Nafaty zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar, yana mai cewa kwamitin ya ƙunshi mambobin da aka zaɓo bisa kwazo, aminci da biyayyarsu.
Mambobin sun haɗa da: Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko Ta Jihar Gombe Dr. Abdulrahman Shuaibu, da Babban Sakataren Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Gombe (Go-Health) Dokta Abubakar Musa, da Dr. Mohammed Garba Buwa daga Ma’aikatar Lafiya, da Architect. Yakubu Mamman daga Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri, da Mohammed Bappa daga Hukumar Kula da Harkokin Kiwon Lafiya ta Jihar Gombe.
Sauran sun haɗa da QS Ahmed Mohammed Kabir, Mai Bada Shawara kan sayayyan kayayyaki, da Misis Rose Andrew daga ma’aikatar lafiya, da kuma Pharmacist Jalo Ibrahim, Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya wanda zai kasance Sakataren kwamitin.
Aikace-aikacen kwamatin sun haɗa da yin cikakken nazari game da ma'aikatan lafiyan jihar don magance matsalolin yadda ake tura ma'aikata wuraren aiki a matakai daban-daban a jihar.
Haka nan an ɗorawa kwamitin alhakin bada shawarar ɗaukar matakan gaggawa na cike giɓin da ake samu a fannin kiwon lafiya, da tantance ayyukan da ake gudanarwa a fannin kiwon lafiya, da tantance buƙatun muhimman cibiyoyin kiwon lafiyan da ake buƙata a jihar, da kuma bada shawarar yadda za a kafa su.
Kwamitin, wadda ke da wa'adin aiki na kwanaki 30, zai duba al'amuran kiwon lafiyan don inganta sashin, tare da bada duk wasu shawarwarin da suka dace.
Gwamna Inuwa ya bayyana kwarin gwiwar samun nasarar ayyukan kwamitin da zai gudanar da wannan muhimmin aiki, inda ya buƙaci mambobin kwamitin su yi aiki da kwarewarsu don inganta fannin lafiyan Jihar Gombe.
Ana sa ran gabatar da sakamakon bincike da shawarwarin kwamitin ta cikin cikakken rahoton da zai gabatar a karshen wa'adin da aka ɗibar masa.
Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment