GWAMNA INUWA YA LASHE KYAUTAR GWARZON GWAMNA NA JARIDAR THE SUN NA 2023
8/01/2024
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gwamnan Na Jaridar The Sun Na 2023
...Inda Yace Karramawar Za Ta Ƙarfafa Masa Gwiwa Wajen Kara Ƙaimi
...Yana Mai Sadaukar Da Karramawar Ga Gombawa
An zabi Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, a matsayin gwarzon Gwamnan na Kamfanin Jaridar The Sun Publishing Limited, Mai wallafa jaridun Daily Sun, da Saturday Sun, Sunday Sun da kuma Sporting Sun.
Manajan Daraktan kamfanin, Mr Onuoha Ukey ne ya miƙa sanarwar zaɓin da aka yiwa gwamnan, yayin da ya jagoranci sauran jami’an gudanarwansa da suka haɗa da Edita Ihenacho Nwonsu da shugabar sashin ayyukan jaridar a Arewa Folashade Adetotu zuwa wata ziyara a masauƙin Gwamnan na Gombe dake Abuja.
“Mun zo ne don sanar da kai cewa Majalisar Editocin Jaridar The Sun Publishing Limited, bayan bin tsattsauran tsarin tantancewa, ta kai ga zaɓanka a matsayin wanda ya lashe kyautar Gwarzon Gwamnan jaridar na 2023.
Manajan Daraktan ya sanar da Gwamnan cewa Majalisar Editocin jaridar ta yanke shawarar ba shi lambar yabon Gwarzon Gwamnan ne bisa la'akari da kyakkyawan shugabancinsa na hangen nesa da kuma irin nasarorin da ya samu ta fuskar samar da ababen more rayuwa, da kiwon lafiya, da ilimi, da inganta muhalli, da samar da ruwan sha da gina jama'a da dai sauransu.
Yace nazari da bincikensu ya nuna cewa Gwamna Inuwa ya yi zarra da fintinkau ga sauran gwamnoni takwarorinsa.
Mr Ukey ya bayyana cewa an keɓe kyautar ta The Sun ce ga duk Gwamnan da ya fi taka rawar gani; wanda gwamnatinsa ta yi tasiri mai inganci ga rayuwar al'umma.
Wasiƙar sanarwar tace “Wannan zaɓin da aka yi maka ya zo ne bisa cancanta saboda irin nasarorin da ka samu a tsawon lokacin da ka kasance Gwamnan Jihar Gombe, mutane da yawa suna ƙiranka a matsayin Gwamna mai hangen nesa, kuma wannan halin ya nuna ƙarara a shekarun da ka yi a matsayin gwamnan Jihar Gombe ".
Manajan Daraktan ya taya Gwamnan murnar zaɓen da aka yi masa a matsayin gwarzon Gwamnan The Sun na 2023, kana ya gayyace shi a hukumance zuwa bikin karramawa da bada kyautar a ranar 17/2/2024 a Eko Hotel and Suites, dake Victoria Island a Jihar Legas.
Da yake karɓar zabin, Gwamna Inuwa Yahaya ya godewa kamfanin jaridar bisa ganin irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, yana mai bayyana karramawar a matsayin ba ga shi kaɗai ba, har ma da tawagarsa da ɗokacin al’ummar Jihar Gombe.
Yace “Wannar karramawa za ta zaburar da mu wajen ƙara kaimi don samar da ci gaba ga al’ummar Jihar Gombe, kuma za mu yi nasarar sauya Gombe fiye da yadda muka same ta.”
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa tana samar da ingantaccen shugabanci ga al’umma ne ta hanyar kyakkyawan kundin ci gaban Jihar Gombe na shekaru 10 daga (2021-2030) da nufin kawo sauyi a jihar nan da shekaru 10 masu zuwa, tare da ɗora ta kan turbar ci gaba mai ɗorewa.
“Mun shigo da kyakkyawar manufa, kuma mun tsara turbar da za ta kaimu ga gaci, kuma muna farin ciki da yadda ake yabawa kyawawan nasarorin da muka samu,” in ji Gwamna Inuwa.
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment