GOMNAN GOMBE: ZAMU HADA HANNU DA ABOKAN HULDAR CIGABA DON INGANTA MULKI DON DACEWA DA BUKATUN AL'UMMAR MU
8/01/2024
Gwamnan Gombe: "Zamu Haɗa Hannu Da Abokan Hulɗar Ci Gaba Don Inganta Mulki Ya Dace Da Buƙatun Al'ummar mu.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na haɗa kai da abokan huldar ci gaba don daidaita harkokin mulki da buƙatun al'ummomin yankunan karkara.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Wakiliyar shirin PROPCOM Plus na ƙasa, shirin da ƙasar Burtaniya ke tallafawa Dr. Adiya Ode a masauƙin Gwamnan Jihar Gomben dake Abuja.
Da yake tsokaci kan k
undin ci gaban jihar na tsawon shekaru 10, wanda aka yiwa laƙabi da DEVAGOM, wadda ya samo asali daga buƙatun al'ummomi da aka tantance kafin ma zuwansa ofis a 2019, Gwamnan ya jaddada buƙatar samar da dabarun haɗin gwiwa don tabbatar da samun ci gaba mai ɗorewa wadda har ƴan baya za su mora.
“A Jihar Gombe muna da kyakkyawar manufa, muna aiki tare da kundinmu na ci gaba wadda ya zayyana manufofinmu na hangen nesa da muka tsara tun kafin mu zo mulki a 2019.
“Ba mu da wani zaɓi da ya wuce haɗa kai da ƙungiyoyi irin naku masu muradun da suka dace da buƙatun al'ummarmu. Dole ne mu yi hakan ba tare da wani ɓata lokaci ba, kuma mu yi shi da kyau don barin gado mai ɗorewa.”
Gwamnan yace wassu daga cikin abubuwan da PROPCOM Plus ta mayar da hankali a kai sun yi daidai da muradun gwamnatinsa, musamman abin da ya shafi kyautata yanayi da bunƙasa kiwo.
Yace ganin yadda Jihar Gombe ke tsakiyar Arewa Maso Gabas, da shirinta na farfaɗo da muhalli; Gombe Goes Green (3G) da kuma gandun kiwo na Wawa-Zange, babu wata jiha daya kamata PROPCOM Plus ta yi haɗin gwiwa da ita kamar Gombe.”
A Gombe muna da wannan shiri na, Gombe Goes Green (3G) wanda a ƙarƙashinsa muke dasa bishiyoyi akalla miliyan ɗaya duk shekara a ƙoƙarinmu na farfaɗo da muhalli.
Haka kuma muna aiki tare da Bankin Duniya akan wassu shirye-shirye makamantan wannan irin su shirin zamanantar da kiwo da ake ƙira (L-PRES) don haɓakawa da inganta kiwon dabbobinmu da kuma shirin inganta muhalli, noma da samar ruwa (ACReSAL) don haɓaka yadda muke aiwatar da shirinmu na kula da inganta muhalli. Don haka zuwan ku, ya sa dole mu yi haɗin gwiwa don samun riba.”
Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada wajabcin ganin Najeriya ta yi amfani da albarkatun ƙasan da Allah ya huwace mata don dogaro da kai, yana mai bada misali da irin nasarorin da aka samu a ƙasashe kamar China, da Singapore, da kuma Rwanda.
Ya bada shawarar sauyawa daga ƙasar dake ci ma zaune ya zuwa ƙasa mai samar ababen da take buƙata duba da ɗimbin albarkatun ƙasa da yawan jama’a, da kuma tarin basira da Allah ya baiwa ƴan Nijeriya.
"Ni ɗan rajin ganin cewa Najeriya ta yi amfani da baiwar da Allah Ya ba ta ne wajen bunƙasa kanta maimakon dogaro da tallafin da ake samu daga ƙasashen da suka ci gaba ko ƙungiyoyin bada agaji. Allah ya albarkace mu da albarkatun ƙasa, da yawan jama'a da kuma basira. Misali China, da Singapore, da Malaysia, da Indonesiya da kuma Indiya har ma da Ruwanda sun yi amfani da wannan tallafi, kuma a yanzu sun samu babban ci gaba; dole ne ita ma Najeriya ta yi koyi da su.
Tun farko Dr. Adiya Ode ta shaidawa Gwamna Inuwa Yahaya cewa Propcom+ sabon shiri ne na UKAid dake bunƙasa noma da kasuwanci a yankunan karkata da nufin haɓaka tattalin arzikin yankunan da suka yi fama da rikice-rikice da fannin inganta yanayi a Najeriya ta hanyar magance matsalolin muhalli, zamantakewa da tattalin arziƙi a fannonin noma da filaye.
Ta buƙaci haɗin gwiwa da gwamnatin Jihar Gombe a fannin noma da bunƙasa dazuzzuka ta yadda za su amfanar da jama’a, da kuaytata yanayi.
"Shirin ya ƙuduri aniyar tallafawa jama'a, da zamanantar da harkokin noma masu ɗorewa waɗanda za su kyautata yanayi tare da rage hayaƙi mai illa ga muhalli da kuma kare yanayin halittu".
“Za mu yi aiki ne a jihohin Kaduna da Gombe da Adamawa, muma mai da hankali ne kan kiwon lafiyar dabbobi, da tallafawa jama’a da ɓangarori masu zaman kansu don sauƙaƙa zuba jari a harkokin noma, tare da dafawa ƙananan manoma masu ƙaramin karfi kan noman shinkafa da ban ruwa don bunƙasa waɗannan sassa.
Ta ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin PROPCOM Plus da Jihar Gombe zai bunƙasa zuba jari a harkokin noma, tare da haɗa kan jama’a da sassa masu zaman kansu don samun ci gaba mai ma'ana da kyakkyawar makoma ga ci gaba mai ɗorewa a Jihar Gombe
Ismaila Uba Misilli
Banban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment