GOMNAN JIHAR GOMBE INUWA YAHAYA YAYI NASARA A KOTUN KOLI
19/01/2024
Gwamna Inuwa Yahaya Yayi Godiya Ga Allah Bisa Nasarar Da Ya Samu A Kotun Ƙoli
...Yana Mai Bayyana Hukuncin A Matsayin Wanda Ya Tabbatar Da Zaɓin Gombawa
...Kana Ya Yi Alƙawarin Ci Gaba Da Aiki Don Kyautatuwar Jihar Gombe
Mai Girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya yaba da hukuncin Kotun Ƙoli wacce ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18/03/2023.
Da yake tsokaci kan hukuncin da kotun ta yanke kan ƙarar da ɗan takaran Jam’iyyar PDP Muhammad Jibrin Barde, da kuma na African Democratic Congress (ADC) Nafiu Bala suka shigar, kwamitin alkalan mai mambobi biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hukuncin a matsayin wadda ya tabbatar da zaɓin al'ummar Gombe a zaɓen daya gabata.
“Bari in fara da miƙa godiyata ga Allah (SWT) bisa dukkan nasarorin da muka samu tun daga zaɓe zuwa kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe har zuwa Kotun Ƙoli. Hukuncin da kotun kolin ta yanke a yau ba wai nasara ce ta ƙashin kaina da jam’iyyata ba, ta ma tabbatar da zaɓin al’ummar Jihar Gombe da suka yi jerin gwano a zaɓen gwamna na 2023 suka ƙara mana wani wa’adi na shekaru huɗu,” inji Gwamnan.
“Tunda an kammala duk shari’o’in a kotuna, yanzu lokaci ne da za mu mayar da hankali ga ciyar da Jihar Gombe gaba, a wa’adin mulkinmu na farko, mun aiwatar da ayyuka, mun bullo da shirye-shirye, da samar da gyare-gyare da tsare-tsaren da suka inganta rayuwar al’ummarmu. Gwamnan ya ƙara da cewa ina tabbatar muku cewa mun himmatu wajen ganin mun ƙara hidimta muku a karo na biyu a wa’adin mulkinmu na biyu, wajen samar muku da ƙarin ribar demokradiyya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada godiya ga al’ummar Jihar Gombe bisa goyon baya da haɗin kai da suka daɗe suna baiwa gwamnatinsa, wadda yace ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da nasarorin da aka samu a shekaru huɗu da rabi da na gwamnatinsa.
“A madadin ni kaina da mataimakina da muƙarraban gwamnatina da kuma ɗokacin ƴan jam’iyyar APC, ina miƙa godiyarmu ga al’ummar Jihar Gombe bisa addu’o’in da suka yi mana, da goyon baya da haɗin kai da suke ba mu tun daga 2019 zuwa yau, kun bada gudummawa sosai ga nasarori da sakamako masu kyau da muka samu a sassa daban-daban", in ji shi.
Da yake yabawa alkalan Kotun Ƙolin bisa kwazo da jajircewar da suka yi wajen gudanar da shari’ar, Gwamnan ya yabawa tawagar lauyoyinsa bisa ƙoƙarin da suka yi na kare haƙƙin al’ummar Jihar Gombe tun daga kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe har zuwa kotun koli, kana ya yabawa shugabanni da mambobin Jam'iyyar APC mai mulki bisa goyon bayan da suka nuna a tsawon wannar tafiya.
Gwamnan ya kuma miƙa gayyata ga ‘yan jam’iyyun adawa musamman waɗanda suka shigar da kararraki a kotuna, inda yace, “Gombe ba ta wani mutum ko jam’iyya ba ce, ba tare da la’akari da wani bambanci ba, jihar ta mu ce baki ɗaya.
Ina ƙira ga ɗokacin ‘yan adawa su zo su haɗa kai da mu wajen yin wannan aiki mawuyaci don mu ciyar ga Gombe gaba. Yayinda wannar shari’a ta kawo ƙarshe, babu wanda ya ci nasara ko ya yi asara, mu haɗa kai don ciyar da jiharmu gaba".
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment