SHUGABAN KUNGIYAR GWAMNONI NA AREWA YA ZIYARCI MINISTOCIN TSARO DON KARFAFA HADIN GWIWA

 22/01/2023 

Muhammadu Inuwa Yahaya Governor of Gombe State

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Inuwa Yahaya, Ya Ziyarci Ministocin Tsaro Don Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Kan Sha'anin Tsaro 


Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa Kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya kai ziyara zuwa hedkwatar tsaro ta ƙasa dake Abuja, inda ya gana da ministan tsaro Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar da takwaransa, ƙaramin ministan tsaro Mohammed Bello Matawalle. 


Shugabannin uku, waɗanda suka yi ganawar sirri, sun tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa baki ɗaya, musamman ta fuskar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya dana jihohi don ƙarfafa matakan tsaro, musamman a Arewa da ma Najeriya baki ɗaya. 

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya yi fice bisa namijin ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Gombe, a koda yaushe yana ƙoƙarin ganin an samar da tsarin bai ɗaya na tinkarar matsalar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi wajen inganta al'amuran tsaro. 


Ismaila Uba Misilli 

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

mekefaruwa.blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

GWAMNATIN JAHAR GOMBE TA DAU MA'AIKATA SAMA DA MUTUM DARI HUDU DON AIKIN BIOMETRIC

GOV INUWA GIVES OUT GOMBE SSG's DAUGHTER, SUMAYYA IN MARRIAGE

GWAMNA INUWA YA HASKAKA NAJERIYA AMATSAYIN GWARZON SHEKARA