Posts

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR GOMBE BARR SANI A.A HARUNA YA GWANGWAJE MA'AIKATA TAREDA KANSILOLI DA NA'URAR AIKI NA ZAMANI

 DIGITAL ALGON CHAIRMAN ✊ SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR GOMBE BARR SANI A.A HARUNA YA GWANGWAJE MA'AIKATA TAREDA KANSILOLI DA NA'URAR AIKI NA ZAMANI A ƙoƙarin shugaban ƙaramar hukumar Gombe na sauya fasalin aiki zuwa anfani da fasahar zamani ALGON Barr. Sani Ahmad ya gwangwaje ma'aikatan ƙararamar hukumar Gombe da kansilolinshi da na'urar aiki ta zamani. Acewar shugaban ƙaramar hukumar,  yanzu muna lokacin da ake ayyuka da kayan aiki na fasahar zamani don haka muma dole mu sauya  zuwa amfani da na'urori a karamar hukumar Gombe. Daga shigarsa ofis zuwa yanzu shugaban ƙaramar hukumar ya kawo sauye sauye na cigaba musamman a ma'aikatar wanda yasa Ma'aikatan ƙaramar hukumar suke masa laƙabi da 'DIGITAL ALGON CHAIRMAN' mekefaruwa.blogspot.com

GWAMNA INUWA YA HASKAKA NAJERIYA AMATSAYIN GWARZON SHEKARA

Image
 Fabrairu 18, 2024 Kyautar Jarida ta Sun: Sannan Inuwa Yahaya Ya Haska A Matsayin Gwamnan Shekara Makwanni biyu kacal da lashe kyautar Gwarzon Gwamnan Jihar Gombe, (Education), Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya sake zama Gwamnan Jihar Gombe na Shekarar 2023 a wani biki da aka gudanar a Eko Hotel and Suites, Victoria Island. , Lagos. Gwamna Inuwa Yahaya, ya haskaka sosai yayin da ake karanto sharhin da ya rubuta kafin gabatar da kyautarsa. Halayensa na ban mamaki a matsayinsa na jagora abin koyi an yaba da babbar murya. An karrama lambar yabon ne a madadin Mai Girma Mataimakin Gwamna Dr. Manassah Daniel Jatau tare da Hon. Ministan Sufuri, Sen. Saidu Ahmed Alkali. The Sun Publishing Limited, masu buga jaridun Daily Sun, Saturday Sun, Sunday Sun da Sporting Sun, na daya daga cikin manyan labaran da ake yadawa a Najeriya da sama da shekaru ashirin na aikin jarida mai inganci da inganci a Najeriya. Manajan daraktan yada labarai, Mista Onuoha Ukey, ya bayyana cewa hukumar e...

GWAMNATIN JAHAR GOMBE TA DAU MA'AIKATA SAMA DA MUTUM DARI HUDU DON AIKIN BIOMETRIC

Image
 Fabrairu 22, 2024 Gyaran Ma'aikatan Gwamnati: Gombe Ta Dau Ma'aikata Sama Da 400 Aikin Na'urar Halartar Ma'aikata. ...Kamar yadda Gwamna Inuwa Yahaya ya kaddamar da horas da masu kula da biometric ... "Ba'a Nufin Tsarin Halitta Don Yin Farautar Ma'aikatan Gwamnati ba" - NLC Gwamnatin Jihar Gombe ta dauki ma’aikata sama da 400 na ‘Biometric Attendance Supervisors (BAS)’ domin su rika gudanar da ayyukan sama da na’urorin Halartar Jihohi 4,000 da aka girka a wasu ma’aikatun Jihohi da na Kananan Hukumomi da nufin bunkasa ayyuka da inganci a Ma’aikatan Jihar. Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya CON ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da horon kwana 1 ga masu kula da su 305 wadanda aka zabo kwanan nan bayan an tantance su. Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya nanata cewa aiwatar da tsarin biometirika a cikin ma’aikatan gwamnati na da matukar muhimmanci wajen zakulo ma’aikatan bogi wadanda suka dade suna sanya w...

GOV INUWA GIVES OUT GOMBE SSG's DAUGHTER, SUMAYYA IN MARRIAGE

Image
 3rd February,  2024 Governor Inuwa Gives Out Gombe SSG's Daughter,  Sumayya in Marriage  Governor Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, led a state government delegation to partake in the nuptial rites of Sumayya Ibrahim Abubakar Njodi, daughter of Professor Ibrahim Abubakar Njodi, the Secretary to the Gombe State Government. The wedding fatiha between Sumayya Njodi and Jamilu Ibrahim took place at the Kaltungo Central Mosque, and was presided by the Chief Imam, Muhammad Isa Imam who sealed the union with the pronouncement of a dowry of one hundred thousand Naira (100,000). Governor Inuwa Yahaya served as the Waliy for the bride, Sumayya, while Dr. Muhammad Bello took on the role of Wakil for the groom, Jamilu. The occasion was witnessed by  dignitaries and other well- wishers including speaker Abubakar Luggerewo, political figures, members of academia from various tertiary institutions within and beyond Gombe State, as well as representatives of the traditional institu...

GOMNAN JIHAR GOMBE YA KAFA KWAMITIN KARTAKWANA DON FARFADO DA BANGAREN LAFIYA

Image
 23/01/2024  Gwamnan Jihar Gombe Ya Kafa Kwamitin Kartakwana Don Farfaɗo Da Ɓangaren Lafiya  Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya kafa kwamitin farfaɗo da fannin kiwon lafiya a jihar, inda Farfesa Aliyu Usman El-Nafaty zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba.  Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar, yana mai cewa kwamitin ya ƙunshi mambobin da aka zaɓo bisa kwazo, aminci da biyayyarsu.  Mambobin sun haɗa da: Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko Ta Jihar Gombe Dr. Abdulrahman Shuaibu, da Babban Sakataren Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Gombe (Go-Health) Dokta Abubakar Musa, da Dr. Mohammed Garba Buwa daga Ma’aikatar Lafiya, da Architect. Yakubu Mamman daga Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri, da Mohammed Bappa daga Hukumar Kula da Harkokin Kiwon Lafiya ta Jihar Gombe.  Sauran sun haɗa da QS Ahmed Mohammed Kabir, Mai Bada Shawara kan sayayyan kayayyaki, da...

SHUGABAN KUNGIYAR GWAMNONI NA AREWA YA ZIYARCI MINISTOCIN TSARO DON KARFAFA HADIN GWIWA

Image
 22/01/2023  Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Inuwa Yahaya, Ya Ziyarci Ministocin Tsaro Don Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Kan Sha'anin Tsaro  Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa Kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya kai ziyara zuwa hedkwatar tsaro ta ƙasa dake Abuja, inda ya gana da ministan tsaro Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar da takwaransa, ƙaramin ministan tsaro Mohammed Bello Matawalle.  Shugabannin uku, waɗanda suka yi ganawar sirri, sun tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa baki ɗaya, musamman ta fuskar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya dana jihohi don ƙarfafa matakan tsaro, musamman a Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.  Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya yi fice bisa namijin ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Gombe, a koda yaushe yana ƙoƙarin ganin an samar da tsarin bai ɗaya na tinkarar matsalar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi wajen inganta al'amuran tsaro. ...

GOMNAN JIHAR GOMBE INUWA YAHAYA YAYI NASARA A KOTUN KOLI

Image
 19/01/2024  Gwamna Inuwa Yahaya Yayi Godiya Ga Allah Bisa Nasarar Da Ya Samu A Kotun Ƙoli ...Yana Mai Bayyana Hukuncin A Matsayin Wanda Ya Tabbatar Da Zaɓin Gombawa  ...Kana Ya Yi Alƙawarin Ci Gaba Da Aiki Don Kyautatuwar Jihar Gombe  Mai Girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya yaba da hukuncin Kotun Ƙoli wacce ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18/03/2023.  Da yake tsokaci kan hukuncin da kotun ta yanke kan ƙarar da ɗan takaran Jam’iyyar PDP Muhammad Jibrin Barde, da kuma na African Democratic Congress (ADC) Nafiu Bala suka shigar, kwamitin alkalan mai mambobi biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hukuncin a matsayin wadda ya tabbatar da zaɓin al'ummar Gombe a zaɓen daya gabata.  “Bari in fara da miƙa godiyata ga Allah (SWT) bisa dukkan nasarorin da muka samu tun daga zaɓe zuwa kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe har zuwa Kotun Ƙoli. Hukuncin da kotun kolin ta yanke a y...