Kasuwar neman Aure
ABIN DAI FA LALUBE NE ! Kasuwar ci-da-addini sai habaka ta ke yi a shafukan Social Media, sai ka ga mutum ya dage kullum shine fadakarwa da wa`azi a shafukan sada zumunta, ba ga mazan ba, ba ga matan ba ! Babban ma abin da zai fi ba ka mamaki shine; an wayi gari ma, kowa shi yake dora kansa a sikeli, ya fitar da sakamakon cewa; shi nagari ne ! Ka gan ta tana post kamar haka:- Wanda ya yi dace da mace tagari, ya gama dacen aure ! Ko ka gan shi yana yin post kamar haka:- Idan kina son jindadin aure ki samu Ustazu ! Yawancin wadannan `yan kiran kasuwa ne, hakikanin jindadin aure; shine ka auri mai son ka tsakani da Allah, kuma domin Allah, matukar dai ba mai baiyana fasikanci ba ne, kuma yana yin aiyukansa na ibada gwargwadon iko ! Soyaiya domin Allah, tsakani da Allah, ita ce take inganta zamantakewar aure, ta samar da salihan iyali, amma soyaiyar da ba don Allah ba, ita take karewa da yin nadama ! Dan uwa da `yar uwa, ku yawaita rokon Allah da ya datar da ku da abokan zama nagari, ...