MEKE FARUWA

RUSHEWAR GIDA BA DAGA NESA YAKE ZUWA BA✍️✍️✍️
_____________
_____________
Wani matashi ya tambayi abokinshi, ina kake aiki?



Sai yace: wuri kaza.

Abokin yace : Nawa ake baka a wata?

Yace:- 5000.

Sai abokin yace : 5000 kadai? Tayaya zaka rayu da dubu biyar? 

Tun daga wannan ranar abokin ya raina aikinshi, ya nemi a qara mashi albashi, mai gidan yaqi qara mashi, shi kuma ya watsar da aikin.

A da yana aiki, yana samun 5000 a wata, amma yanzu baya aikin komai.

✍️Wata ta tambayi qawarta wace kyauta mijinki ya baki a ranar birthday dinki?
Sai tace bai bani komai ba.
Shine qawar tace : Da gaske kike? Anya kina da daraja a wurinshi kuwa? 

Tunda ta jefa mata wannan bomb din a gida ta fita, da mijin matar nan ya dawo ya tadda ta cikin fushi, suka hau rigima da jayayya daga qarshe ya sake ta.

Daga ina matsalar ta fara? Daga wannan kalmar da qawarta ta gaya mata.

✍️Ance akwai wani mahaifi da yake rayuwa cikin kwanciyar hankali da iyalanshi,  sai abokinshi yace mashi, ya akai danka bai ziyartarka sosai? Anya rashin lokaci ne ko ko dai baya sonka?
Tun daga wannan rana kwanciyar hankalin mahaifin ya qare, ya dawo kallon dukkan abunda danshi yakeyi a matsayin aibi da kuskure, kullum cikin damuwa da rashin godiyar kyautatawar da dandanshi yake mashi.

🌳Tambayoyi ne da zamu iya tsammanin daidai suke, saidai suna iya rusa zamantakewa.

✍️Miyasa baka sayi babbar waya ba?
✍️Miyasa baka mallaki mota ba?
✍️Tayaya zaka riqa jure halayen wannan mutumin?
✍️Tayaya zaka bari ana yi maka wannan abun?

🌳Muna yin wadannan tambayoyin la'alla bisa rashin sani, ko son jin labari, saidai bamu sani ba zasu iya haifar da wasu tambayoyin a zuciyar mai sauraro.

✍️🌹Abunda saqon ya qumsa shine : Karka zamo cikin masu rusa katangar alaqar da take ginanna.

🤝Ka shiga gidan mutane a makance, ka fito a kurmance, babu ruwanka da aibobin cikinsa.

🤝Ba ina wanke kaina bane a lokacin da nake isar da wannan saqon...kuma ba ina nufin ni bana kuskure bane.

Kawai dai nasiha ce nake aikawa zuwa ga kai.

Ina muku fatan alkhairi da kuma barka da safiya...

Comments

Popular posts from this blog

GWAMNATIN JAHAR GOMBE TA DAU MA'AIKATA SAMA DA MUTUM DARI HUDU DON AIKIN BIOMETRIC

GOV INUWA GIVES OUT GOMBE SSG's DAUGHTER, SUMAYYA IN MARRIAGE

GWAMNA INUWA YA HASKAKA NAJERIYA AMATSAYIN GWARZON SHEKARA