Kasuwar neman Aure

 ABIN DAI FA LALUBE NE !

Kasuwar ci-da-addini sai habaka ta ke yi a shafukan Social Media, sai ka ga mutum ya dage kullum shine fadakarwa da wa`azi a shafukan sada zumunta, ba ga mazan ba, ba ga matan ba !

Babban ma abin da zai fi ba ka mamaki shine; an wayi gari ma, kowa shi yake dora kansa a sikeli, ya fitar da sakamakon cewa; shi nagari ne !

Ka gan ta tana post kamar haka:-

Wanda ya yi dace da mace tagari, ya gama dacen aure !

Ko ka gan shi yana yin post kamar haka:-

Idan kina son jindadin aure ki samu Ustazu !


Yawancin wadannan `yan kiran kasuwa ne, hakikanin jindadin aure; shine ka auri mai son ka tsakani da Allah, kuma domin Allah, matukar dai ba mai baiyana fasikanci ba ne, kuma yana yin aiyukansa na ibada gwargwadon iko !

Soyaiya domin Allah, tsakani da Allah, ita ce take inganta zamantakewar aure, ta samar da salihan iyali, amma soyaiyar da ba don Allah ba, ita take karewa da yin nadama !

Dan uwa da `yar uwa, ku yawaita rokon Allah da ya datar da ku da abokan zama nagari, domin mafi yawan mutanen yanzu, kura ce da fatar akuya, amma idan kana neman zabin Allah, sai ya kawo maka abokin zaman nagari, ko kuma idan ya so, ya jarrabi imaninka, sai ya hada ka da wanda macijin kaikayi ne !

Kar dai ku rinka ruduwa da gwanayen tsara posts din wa`azi, abin ba a rubutu ba ne, a tarbiyya da hali ne, shi kuma ba za a gane ba, sai zaman ya hada, don haka; addu`a ita ce kau-da-barar mumini !


Comments

Popular posts from this blog

GWAMNATIN JAHAR GOMBE TA DAU MA'AIKATA SAMA DA MUTUM DARI HUDU DON AIKIN BIOMETRIC

GOV INUWA GIVES OUT GOMBE SSG's DAUGHTER, SUMAYYA IN MARRIAGE

GWAMNA INUWA YA HASKAKA NAJERIYA AMATSAYIN GWARZON SHEKARA