Gomnatin Nigeria na Shirin korar ma'aikatanda Basu cancanta a aiki ba
Gwamnatin tarayya ta nuna alamar tana shirin korar ma'aikata da ba su san makamashin aiki ba - Folashade Yemi-Esan, shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ce ta sanar da hakan ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu - Shugaban ma'aikatan na kasa ta ce wadanda suka cancanta ne kawai za a dauka aiki a hukumomin gwamnatin tarayya Folashade Yemi-Esan, shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, HoS, ta ce za a bullo da tsarin da zai tabbatar wadanda suka dace ne kawai za su samu aikin gwamnatin tarayya. Vanguard ta ruwaito cewa Yemi-Esan ta yi wannan furucin ne a wurin taron Hukumar Yin Sauye-Sauye a ayyukan gwamnati, BPSR, da aka yi a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu a Abuja. DUBA WANNAN: Mekefaruwa.blogspot.com